Saturday, 28 January 2017

ZA A FARA AMFANI HAUSA WAJEN KOYAR DA WASU DARUSSA A MAKARANTU


Gwamnatin tarayya na dubu yiwuwar amfani yaruka da aka fi amfani dasu a Najeriya wajen koyar da darrussan kimiya da fasaha.
Ministan kimiyya da fasaha, Ogbonnaya Onu, ya sanar da haka lokacin da yake tattaunawa da daliban makarantar firaimari na Ekulu dake jihar Enugu.
Ya ce hakan zai taimaka wajen jan ra’ayin dalibai kan muhimmancin da ke tattare da wadannan darussa a makarantu dake fadin kasar nan.
Onu, ya ce bincike da wasu kwararru a kasashen duniya suka gudanar ya nuna cewa amfani da yarukan cikin gida na taimakawa dalibai wajen gane abin da ake koyar da su cikin gaggawa.

Ya ce har ila yau hakan zai taimaka wajen karfafa yarukkan tare da kara musu inganci musamman a fagen koyarwa a fadin Najeriya. Sannan zai kubutar da yarukka daga bata.

SHUGABA MUHAMMADU BUHARI ZAI DAWO NAJERIYA RAN.........


Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa ana kyautata zaton dawowar shugaban kasa Muhammadu Buhari ranar Litinin 6 ga watan Fabrairun shekara ta 2017. 
Mai ba shugaban kasa shawara a kafofin watsa labarai, Femi Adesina, ya bayyana haka ga manema labarai.
Ya ce shugaban na cikin koshin lafiya sabanin yadda aka yi ta yada jita-jitan yana nan mutu kwakwai-rai kwakwai. 

Thursday, 26 January 2017

AN FALLASA WADANDA SUKA HADDASA JITA-JITAR RASHIN LAFIYAR BUHARI


Kafar sadarwa ta DAAR Communications ta zargi wata kungiya ga rahoton da aka kafa a kan karya a shafin Facebook ta gidan sadarwar da iƙirarin Shugaba Buhari ya mutu a cikin wata asibiti a London.

Gidan yada labarai ya furta cewa, mutuwar jita-jitar shugaba Buhari wata zaton tunanin marubutar ne kawai.

Wata rohoto daga kamfanin sadarwa na DAAR Communications ta ce ta nisanci wannan rahotanni da ta auku a karshen mako da ta gabata cewa shugaba Muhammadu Buhari ya mutu a wata asibiti a London.

JAM'IYYAR APC TA GAYYACI SHEHU SANI KAN SUKAR BUHARI DA YA YI


Shugaban jam’iyyar APC na kasa baki daya, Cif John Odigie-Oyegun ya rubuta wata wasika a yammacin jiya wanda za’a aika ga sanatan na gayyatar sa hedkwatan jam’iyyar a Abuja don tattauna sukarsa ga yadda shugaban kasa ya dauki al’amarin zargin rashawa da ake yi a kan Lawal.

Kimanin wata daya da ya wuce, kwamitin kula da wadanda rikin Boko Haram ta cika dasu na majalisar dattawa karkashin jagorancin Sani ta zargi Lawal da aikata zamba na kwangilar sansanin yan gudun hijira a arewa maso gabas.

A wasikar sa ga majalisa, shugaban kasa yayi mamakin yadda akayi majalisar ta yanke shawarar kira ga cire Lawal alhalin ba’a taba kiran babban sakataren na tarayya don kare kansa ba.

HOTUNAN ARANGAMA DA AKA SAMU TSAKANIN 'YAN SHI'A DA 'YAN SANDA


Kadan daga cikin hotunan arangama da aka samu tsakanin 'yan sanda da mabiya akidar shi'a a babban birnin tarayya Abuja.
Allah ya kyauta...
Akwai bukatar daukan matakan da suka kamata...

BUHARI YA SAKEMAGANA AKAN 'YAN TA'ADDAN NIGER DELTA


Shugaba Muhammad Buhari ya roki mayakan tsagerun Niger Delta da ke kai hare hare kan bututun mai kan su zo a zauna kan teburin shawarwari don ganin an samu zaman lafiya mai dorewa a yankin.

Buhari ya yi wannan kiran ne a lokacin da. Ministan Abuja, Muhammad Bello ya jagoranci Kiristocin da ke birnin wurin kai masa ziyara na bikin Kirismeti inda ya ce zaman sulhu zai ba bangarorin damar cimma yarjejeniya kan yadda za a raba arzikin man fetur din.

Monday, 16 January 2017

WASU SABBIN 'YAN TA'ADDA SUN GINDAYAWA SHUGABA BUHARI SHARUDDA


Wasu sababbin Tsageru sun ba Shugaban Kasa Muhammadu Buhari nan da makonni biyu ya sauke Shugaban EFCC Ibrahim Magu da kuma Sakataren Gwamnati Babachir Lawal.

Wasu sababbin Tsageru da suka bayyana sun ba Shugaban Kasa Muhammadu Buhari nan da makonni biyu ya sauke Shugaban Hukumar EFCC Ibrahim Magu da kuma Sakataren Gwamnatin Sa, Babachir David Lawal.

Tsagerun dai sun ce idan har lokacin da suka bada ya cika kuma ba a aiwatar da hakan ba, to ba shakka za su tada rikici a Kasar. Mai magana a madadin Kungiyar, Hart Bradford yace za su yi zanga-zanga a ko ina cikin Biranen Kasa idan Shugaba Buhari bai yi hakan ba.

Tsagerun dai sun ce idan har lokacin da suka bada ya cika kuma ba a aiwatar da hakan ba, to ba shakka za su tada rikici a Kasar.

Mai magana a madadin Kungiyar, Hart Bradford yace za su yi zanga-zanga a ko ina cikin Biranen Kasa idan Shugaba Buhari bai yi hakan ba.