Saturday, 28 January 2017

ZA A FARA AMFANI HAUSA WAJEN KOYAR DA WASU DARUSSA A MAKARANTU


Gwamnatin tarayya na dubu yiwuwar amfani yaruka da aka fi amfani dasu a Najeriya wajen koyar da darrussan kimiya da fasaha.
Ministan kimiyya da fasaha, Ogbonnaya Onu, ya sanar da haka lokacin da yake tattaunawa da daliban makarantar firaimari na Ekulu dake jihar Enugu.
Ya ce hakan zai taimaka wajen jan ra’ayin dalibai kan muhimmancin da ke tattare da wadannan darussa a makarantu dake fadin kasar nan.
Onu, ya ce bincike da wasu kwararru a kasashen duniya suka gudanar ya nuna cewa amfani da yarukan cikin gida na taimakawa dalibai wajen gane abin da ake koyar da su cikin gaggawa.

Ya ce har ila yau hakan zai taimaka wajen karfafa yarukkan tare da kara musu inganci musamman a fagen koyarwa a fadin Najeriya. Sannan zai kubutar da yarukka daga bata.

No comments:

Post a Comment