Monday, 2 January 2017

HOTUNAN KUNAR BAKIN WAKE


Hotunan harin kunar bakin wake a kusa da ofishin Kwastom dake 'Custom Area' Maiduguri babban birnin jihar Borno.
Kakakin rundunar yan sandan jihar, Victor Isuku ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce an kai harin ne a yankin "Custom Area" dake cikin birnin jihar, sai dai ya ce binciken farko ya nuna cewa maharan ne kadai suka mutu.
Harin wanda ya auku da misalin karfe goma na daren jiya, na zuwa ne a lokacin da ake murnar shiga sabuwar shekara 2017 a yau Lahadi.

No comments:

Post a Comment