Saturday, 28 January 2017

ZA A FARA AMFANI HAUSA WAJEN KOYAR DA WASU DARUSSA A MAKARANTU


Gwamnatin tarayya na dubu yiwuwar amfani yaruka da aka fi amfani dasu a Najeriya wajen koyar da darrussan kimiya da fasaha.
Ministan kimiyya da fasaha, Ogbonnaya Onu, ya sanar da haka lokacin da yake tattaunawa da daliban makarantar firaimari na Ekulu dake jihar Enugu.
Ya ce hakan zai taimaka wajen jan ra’ayin dalibai kan muhimmancin da ke tattare da wadannan darussa a makarantu dake fadin kasar nan.
Onu, ya ce bincike da wasu kwararru a kasashen duniya suka gudanar ya nuna cewa amfani da yarukan cikin gida na taimakawa dalibai wajen gane abin da ake koyar da su cikin gaggawa.

Ya ce har ila yau hakan zai taimaka wajen karfafa yarukkan tare da kara musu inganci musamman a fagen koyarwa a fadin Najeriya. Sannan zai kubutar da yarukka daga bata.

SHUGABA MUHAMMADU BUHARI ZAI DAWO NAJERIYA RAN.........


Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa ana kyautata zaton dawowar shugaban kasa Muhammadu Buhari ranar Litinin 6 ga watan Fabrairun shekara ta 2017. 
Mai ba shugaban kasa shawara a kafofin watsa labarai, Femi Adesina, ya bayyana haka ga manema labarai.
Ya ce shugaban na cikin koshin lafiya sabanin yadda aka yi ta yada jita-jitan yana nan mutu kwakwai-rai kwakwai. 

Thursday, 26 January 2017

AN FALLASA WADANDA SUKA HADDASA JITA-JITAR RASHIN LAFIYAR BUHARI


Kafar sadarwa ta DAAR Communications ta zargi wata kungiya ga rahoton da aka kafa a kan karya a shafin Facebook ta gidan sadarwar da iƙirarin Shugaba Buhari ya mutu a cikin wata asibiti a London.

Gidan yada labarai ya furta cewa, mutuwar jita-jitar shugaba Buhari wata zaton tunanin marubutar ne kawai.

Wata rohoto daga kamfanin sadarwa na DAAR Communications ta ce ta nisanci wannan rahotanni da ta auku a karshen mako da ta gabata cewa shugaba Muhammadu Buhari ya mutu a wata asibiti a London.

JAM'IYYAR APC TA GAYYACI SHEHU SANI KAN SUKAR BUHARI DA YA YI


Shugaban jam’iyyar APC na kasa baki daya, Cif John Odigie-Oyegun ya rubuta wata wasika a yammacin jiya wanda za’a aika ga sanatan na gayyatar sa hedkwatan jam’iyyar a Abuja don tattauna sukarsa ga yadda shugaban kasa ya dauki al’amarin zargin rashawa da ake yi a kan Lawal.

Kimanin wata daya da ya wuce, kwamitin kula da wadanda rikin Boko Haram ta cika dasu na majalisar dattawa karkashin jagorancin Sani ta zargi Lawal da aikata zamba na kwangilar sansanin yan gudun hijira a arewa maso gabas.

A wasikar sa ga majalisa, shugaban kasa yayi mamakin yadda akayi majalisar ta yanke shawarar kira ga cire Lawal alhalin ba’a taba kiran babban sakataren na tarayya don kare kansa ba.

HOTUNAN ARANGAMA DA AKA SAMU TSAKANIN 'YAN SHI'A DA 'YAN SANDA


Kadan daga cikin hotunan arangama da aka samu tsakanin 'yan sanda da mabiya akidar shi'a a babban birnin tarayya Abuja.
Allah ya kyauta...
Akwai bukatar daukan matakan da suka kamata...

BUHARI YA SAKEMAGANA AKAN 'YAN TA'ADDAN NIGER DELTA


Shugaba Muhammad Buhari ya roki mayakan tsagerun Niger Delta da ke kai hare hare kan bututun mai kan su zo a zauna kan teburin shawarwari don ganin an samu zaman lafiya mai dorewa a yankin.

Buhari ya yi wannan kiran ne a lokacin da. Ministan Abuja, Muhammad Bello ya jagoranci Kiristocin da ke birnin wurin kai masa ziyara na bikin Kirismeti inda ya ce zaman sulhu zai ba bangarorin damar cimma yarjejeniya kan yadda za a raba arzikin man fetur din.

Monday, 16 January 2017

WASU SABBIN 'YAN TA'ADDA SUN GINDAYAWA SHUGABA BUHARI SHARUDDA


Wasu sababbin Tsageru sun ba Shugaban Kasa Muhammadu Buhari nan da makonni biyu ya sauke Shugaban EFCC Ibrahim Magu da kuma Sakataren Gwamnati Babachir Lawal.

Wasu sababbin Tsageru da suka bayyana sun ba Shugaban Kasa Muhammadu Buhari nan da makonni biyu ya sauke Shugaban Hukumar EFCC Ibrahim Magu da kuma Sakataren Gwamnatin Sa, Babachir David Lawal.

Tsagerun dai sun ce idan har lokacin da suka bada ya cika kuma ba a aiwatar da hakan ba, to ba shakka za su tada rikici a Kasar. Mai magana a madadin Kungiyar, Hart Bradford yace za su yi zanga-zanga a ko ina cikin Biranen Kasa idan Shugaba Buhari bai yi hakan ba.

Tsagerun dai sun ce idan har lokacin da suka bada ya cika kuma ba a aiwatar da hakan ba, to ba shakka za su tada rikici a Kasar.

Mai magana a madadin Kungiyar, Hart Bradford yace za su yi zanga-zanga a ko ina cikin Biranen Kasa idan Shugaba Buhari bai yi hakan ba.

RUNDUNAR SOJI SUN GANO MAKABARTAR BOKO HARAM


Rundunar soji sun gano makabartan Yan Boko Haram; da gawawwaki.

Rundunar sojin Najeriya na Operation Lafiya Dole sun gano wani makabarta da yan ta’addan Boko Haram ke amfani dashi gurin binne wasu daga cikin yan mambobin su.

A cewar Birgediya Janar Sani Kukasheka Usman a wata sanarwa a ranar Lahadi, 15 ga watan Janairu yace rundunar sojin Oeration Lafiya Dole ne suka gano kaburburan.

“Rundunar bataliya 119 na Operation LAFIYA DOLE yayin sintiri a yau, sun ci karo da kaburburan yan ta’addan Boko Haram da suka tsere da raununkan bindiga suka kuma mutu bayan wani arangarama a ranar 13 ga watan Janairu 2017 sannan kuma aka binne su a cikin kaburbura masu zurfi.

Thursday, 12 January 2017

WANI YA MA 'YAR SA FYADE


Wata mata mai suna Olamide Bola ta zargi mai gidan ta da yin ma’amala da yar su mai shekara 11 da haihuwa. A inda matar ke neman kotu ta raba masu aure.

Ita wannan matar da mijinta suna da shekara 15 da aure, amma matar ta furta cewa kotu ta raba masu aure sanadiyar danye aiki da mijin ya aikata.

'YAN MATA SUN NUNA KIN AMINCEWA KAN DOKAR KAYYADE YAWAN KAYAN AURE A KANO

'Yan mata a karamar hukumar Dambatta ta jihar Kano a Najeriya, sun ce ba su ji dadin dokar da masu ruwa da tsaki a karamar hukumar suka yi ba, wadda ta kayyade kayan aure.
A makon da ya gabata ne dai masu fada aji a Dambatta suka fidda wani kundin doka wanda ya takaita yawan wahalhalun da ake yi wajen aure.

Kundin dokar mai shafi biyar ya wallafa sabon tsarin aure kamar haka:
  • Saukaka kayan aure: Hijabi da mayafi da takalmi da jaka da sarka da warwaro da dan kunne da kuma man gashi guda biyu-biyu.
  • Saiti dai-dai na Jagira da jambaki da hoda da agogo.
  • Turare guda uku
  • Sabulu saiti uku
  • Tufafi da man shafawa kala shida kowanne
  • Akwati daya ko biyu

Dokar ta kuma haramta wasu al'adu kamar haka:
  • Zancen dare
  • Kai lefe da mata ke yi
  • Kayan sa-rana
  • Kade-kade lokacin biki da ke haifar da cakuduwar maza da mata
  • Kamun amarya da ango
  • Bayar da kudin abincin biki
  • Kai Gara
  • Budar kai
  • Da kuma hana taron motocin daukar amarya

Image captionDokar ta kuma hana al'adar kade-kade lokacin biki da ke haifar da cakuduwar maza da mata


Yanzu dai samari na karamar hukumar bakinsu har kunne domin sun ce abin da suka dade suna jira ne.
Wani sauraryi a garin na Dambatta ya shaida wa BBC cewa "gaskiya wannan sauki ne ya zo mana domin da akwai wani kudin uwar miji da uban miji amma yanzu duk babu wadannan."
To sai dai 'yan mata sun ce ba su ji dadin dokar ba domin a cewrsu hakan zai sanya kimarsu ta zube a idanun mazaje.
"Gaskiya ban ji dadin wannan doka ba saboda har ta kai ga samarin garin nan marasa mutunci na cewa da dubu bakwai za ka kwashi mata biyu." in ji wata mazauniyar Dambatta.
A bangaren malaman musulunci kuwa, wasu sun ce dokar ba ta dace ba domin a cewarsu babu inda aka nuna kayyade abun da za a ba wa mace lokacin aurenta.

Sharhi, Usman Minjibir

Za a dai a iya cewa ba wannan ne karon farko da wata al'umma kan kirkiro dokar takaice hidimar aure ba a arewacin Najeriya.
Garuruwa daban-daban sun sha kirkiro irin wannan dokar amma sai a wayi gari ba ta aiki.
Ko a garin Dambattan ma, an ce wannan shi ne karo na uku da ake shimfida irin wannan dokar.
Wasu dai na alakanta rashin tasirin da kokar kan yi da wuce gona da iri da masu hannu da shuni ke yi.
Yawancin lokuta, a kan fara karya irin wadannan dokokin ne daga gidajen masu fada aji da masu ido da tozali musamman a lokacin bukukuwansu ko kuma na 'ya'yansu.
Arewacin Najeriya dai na fama da matsalolin rayuwa da suka hada da talauci da yawan sakin mata al'amarin da ke janyo yawaitar yara marayu a yankin.
Sai dai kuma masu sharhi na ganin irin wannan mataki ba zai kai ga samar da mafita ba illa iyaka ma dai ya sanya maza yin auri saki.
To amma kuma wasu na ganin bisa ga dokar da al'ummar Dambatta suka fitar, akwai masu sanya ido kan yadda auren zai kasance.

HOTUNAN WANI KABARI DA CIYAWARSA BASA BUSHEWA KO DA RANI

An gano wani kabari da ciyawar saman sa baya bushewa a cikin tsawon shekaru...

Tuesday, 10 January 2017

HOTUNAN 'YAR SARKIN KANO DA TA YI SAUKA A SHEKARU 9


Maryam Sanusi (Inna) Mai Shekaru Tara Da Haihuwa 'Yar Mai Martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi ll, Ta Yi Saukar Karatun Al-kur'ani, Inda Aka Yi Bikin Saukar A Ranar Asabar.

Allah ya yiwa rayuwa Albarka...

Monday, 9 January 2017

SHUGABANNIN COCIN KATOLIKA SUN CE BA ZA SU BI UMURNIN CAN BA


Shugaban cocin Katolika, John Cardinal Onaiyekan, ya ce ba zasu bi umurnin addu’an kwana daya da kungiyar gamayyar kiristocin Najeriya watau CAN tayi umurnin ayi game da rayukan da aka rasa a jihar Kaduna ba. 
Yayinda yake bayyana dalilinsa na yin hakan, ya bayyana cewa mabiya Katolika basu bin umurnin CAN. Yace: "Ban yi imani da yin addua wani ranan takamamma ba, kayi addu’a saboda ubangiji ya tsirar da mu ,ba wai lallai a ranan 8 ga watan Junairu ba."
Kafin yanzu, sakataren kungiyar CAN, Dr. Musa Asake ya alanta ranan Lahadi,8 ga watan Junairu 2017 a matsayin ranan makokin dukkan kiristocin da suka rasa rayukansu a jihar Kaduna.
Dr Asake ya kara da cewa dukkan kiristoci su sanya bakin kaya a ranan kuma suyi addu’a sosai ga wadanda suka rasa rayukansu a kudancin Kaduna.
Amma Katolika sunce ba zasu bi umurnin nan ba da bakin shugabansu Onaiyekan. Yace : Ban san abinda zance game da shugabancin CAN ba yanzu saboda cocinmu bata cikin CAN yanzu. Bamu ma san yadda aka zabi sabon shugaban CAN din ba. Saboda haka abinda zan iya yi shine in zauna in sha kallo.
“Ba zan iya ce ma dukkan mambobina su sanya bakaken kaya su zo coci ranan lahadi ba, bamu bin umurnin CAN; kowani coci na da umurnin ta.”

AN TSINCI GAWAR WANI DATTIJO RATAYE A KANO


Rahotanni dake iske mu daga garin Warwarnu a karamar hukumar Gezawa a jihar Kano na cewa da safiyar yau ne aka tsinci gawar wata tsohuwa a rataye a wata bishiya.


Duk da cewa wakilan mu sun ziyarci gurin da abin ya faru, kasantuwar makusanta wannan tsohuwa na halin kidima ba mu sumu tattaunawa da su ba.


Tuni hukumar jami'an kashe gobara da ceton rayuka ta jihar Kano suka dauke gawarta.

HOTON WANI BARAWO DA AKA KONA A NEJA

An Kone Barawon Babur A Garin Bidda Dake Jihar Neja

Saturday, 7 January 2017

KANA BUKATAR KOYON FULATANCI CIKIN SAUKI?



Shirin "MU KOYI FULFULDE" Zai zo muku kamar yadda aka saba, da misalin karfe 6:30pm na yammacin Kowacce Asabar, a Gidan Radio Liberty Megahertz 103.1 zangon FM
Koyi Harshen Fullacin cikin sauki.

Kuma yau shirin zai maida hankali ne kan duba abubuwan da kuka koya a baya, ta hanyar yiwa masu sauraron wannan shirin tambayoyi.

Akwai kyauta da muka tanadarwa duk wadanda ya yi nasara, a wasu tambayoyi.
ZAKU IYA TURO SAKON KU A SHIRIN MU KOYI FULFULDE LIBERTY FM 103.1
TA WHATSAPP AKAN WANNAN LAMBAR 08077673473
KO SHAFIN MU NA FACEBOOK
Mu Koyi Fulfulde Liberty Radio 103.1

WADANDA SUKA CI GASAR ALKUR'ANI SUN SAMU MILIYOYIN NAIRORI, DA KUJERUN HAJJI


Gwamna Aminu Tambuwal ne ya sanar da hakan, a lokacin bukin rufe gasar musabaka karo na  talatin da daya a garin Tambuwal.
Haka Tambuwal ya kara da cewa Gwamnatin jihar Sokoto za ta gina makarantun renon yara na islamiya da wadansu makarantun tsangaya islamiyya da ake gwamaya karatun boko cikin su kimanin dari hudu da tamanin da takwas. Yace za a yi hakan ne domin a gwamaya karatun boko da na kur'ani.




Idan dai baku manta ba kwanan baya gwamnatin jihar ta Sokoto ta daukaka darajar wadansu makarantun islamiyya na al'umma guda goma sha biyar zuwa na mata  domin inganta koyarwa a wadannan makarantu.
Gwamna Tambuwal ya kuma yi alkawarin ci gaba da yin duk abin da ya dace domin bunkasa ilmin addini da kuma sha'anin musabaka a jihar Sokoto.
Haka zalika za a ci gaba da ginawa, gyara da kuma fadada makarantun islamiyya da masallatai a fadin jahar. Ya bayyana cewa bada dadewa ba ya sanyawa wata doka hannu ta amincewa kwamitin zakka da wakafi ya koma hukuma domin inganta ayukkan su, a kuma ragewa wa mabukata wahalhalun yau da kullum. 
Da yake jawabi Mai Alfarma Sarkin Musulmi wanda sarkin yakin Binji Alh Kabiru Usman Abdulwahab ya wakilta, ya ba da tabbacin ci gaba da bada goyon bayan shi wajen inganta shaanin musabaka da hardar Qurani. Ya jinjinawa gwamntin jaha kan kudurinta na ba sashen ilimi kulawar da ya kamata.
A nashi jawabi kwamishinan ilimi na matakin farko da sakandare, Dakta Moh'd Jabbi
Kilgori, ya yabawa gwamntin jihar kan goyon bayan da take bayarwa wajen ingantawa da bunkasa ilimi a jihar, wanda ya sa kwalliya na biyan kudin sabulu kasancewa duk lokacin da yan asalin jihar suka je gasar musabaka sukan dawo da nasara da kyautar da suka ci.
Ya yi kira ga shugabannin kananan hukumomi da su ba jamian musabaka na yankunan su goyon bayan da ya kamata domin a zakulo yara masu hazaka da za su wakilci jahar.
Wadanda suka lashe kyautar gwarzon shekara a  gasar dai sune Lukman Umar daga Wamakko a bangaren maza sai Zainab Aliyu Gidan Kanawa daga Sokoto Ta Kudu? a bangaren mata wadanda suka lashe bangaren hizif sittin da tajweed da tafseer.
Kowannen su dai ya samu kyautar naira miliyan daya da kujerun aikin hajji su da mahaifansu wanda gwamna Tambuwal ya ba su, Mai Alfarma Sultan ya ba namijin babur macen kuma an ba ta gado da kujeru. Suma wadanda suka lashe gasar hizif sittin ba tare da tajweed ba Gwamna Tambuwal ya ba su kujerin makka.
Shi ma wanda ke kula a gasar musabaka, Malam Bello Abdulhakim Galadanci Gwamna ya bashi mota. A yayin da kwamishinan lamurran addini, Mani Maishinko ya ba dukkanin ko'odinetocin musabaka na kananan hukumomi 23 babura domin su ci gaba da gudanar da aikin su yadda ya kamata.
Sauran wadan da suka ci nasara a hizif goma da ishirin da arba'in suma sun samu kyautar kudi.

ZA A KAFA MAKARANTAR SOJI A KATSINA


A wata sanarwa da jami'in hulda da jama'a na ma'aikatar ilimi ta jahar Katsina Alhaji Salisu Lawal Kerau, ya sanyawa hannu ya rabawa manema labarai ta bayyana cewa Gwamna Aminu Bello Masari ya amince da gina makarantu sakandiren sojoji guda biyu ta maza da mata a Katsina.
Sanarwa ta kara da cewa makarantu za'a gina guda a Karamar Hukumar Faskari wadda ta maza ce zalla, a yayin da za'a gina ta 'yan mata a garin Barkiya dake Karamar Hukumar Kurfi. Haka kuma dukkansu na kimiyya ne.
Kamar yadda sanarwa ta ce wadannan makarantu suna karkashin kulawar rundanar  sojojin Nijeriya. Kuma tuni shirye-shirye sun yi nisa na ganin an fara karatu a makaranta 'yanmatan dake garin Barkiya.
Idan za'a iya tunawa a kwanaki baya ne Gwamna Aminu Bello Masari ya amince da kafa makarantar sakandire ta Jami'an Tsaron Farin Kaya Wato (DSS) a Karamar Hukumar Musawa. Daman akwai Sakandiren 'Yan Sanda ta maza dake Karamar Hukumar Mani.

AN KAMA WADANDA SUKA YI GARKUWA DA HIRSE


A watan Nuwamba ne dai wasu suka kama Ambasada Bagudu Hirse Mammam tsohon minista, a daidai kofar gidan Mammam Daura dake Kaduna.

Rahotanni sun nuna cewa jami'an tsaro sun kamo su, tare da muggan makaman da suke amfani dasu wajen aikata mummunan aikin satar mutane.

KOTU TA KWACE SAMA DA DALA MILIYAN 53 DAGA HANNUN DIEZANI

INA 'YAN MATA DA MATAN AURE MASU SON BIRGE MAZAJEN SU

Ga dama ta samu....