This blog is a blog that keeps you informed of local and international news, Events, and Issues, happenings around the world, including entertainments, it breaks the news while its hot.
Saturday, 31 December 2016
HARAMUN NE MUSULMI YA KASHE WANDA YA ZAGI ANNABI
Friday, 30 December 2016
BABACHIR YA KARE KANSA KAN ZARGE-ZARGE
ASALIN BATUN ADDININ RAHAMA SADAU
Rahma Sadau, ta ce tana nan daram a cikin addinin Musulunci.
Jarumar ta bayyana hakan ne sakamakon jita-jitar da ake ta yadawa na cewa ta bar Musulunci bayan an yaudare ta da dalolin miliyoyin kudi na Amurka.
Idan ba a mance ba dai, Rahma Sadau ta koma kasar Amurka ne sakamakon gayyatar da shahararren mawakin kasar Amurka Akon da wasu suka yi mata, sakamakon korar ta da aka yi daga masana'antar fim bayan an zarge ta rungumar wani mawaki mai suna Klassiq a wata kasarsa ta bidiyo.
ZA A RATAYE DAN HAKIMI A KATSINA
An yankewa wani dan Hakimin Katsina hukuncin kisa ta hanyar rataya
Wata babbar Kotu dake Funtua a jihar Katsina ta yankewa, Mu’ammar Tukur dan mai martaba tsohon hakimin Bakori hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa samun shi da laifin kisa.
Kotun ta kuma ce bata da hurumin yin sassauci akan hukuncin.
Tukur mai shekara 32, wanda kuma margayi mahaifin nasa ya wakilci Bakori da Danja a majalisar wakilai ta tarayya, kotu ta same shi da laifin dabawa Shafir Muktar wuka a ranar 21 ga watan Afrelun 2008 a gidan kallo.
Da yake yanke hukunci a ranar Alhamis Alkalin kotun mai Shara'a, Abbas Bawale ya ce kotu ta samu gamsassun shaidu da hujjoji da suka tabbatar da shine yayi kisan.
Hausa Times ta samu bayanin tun bayan faruwar kisan a shekara 2008 Tukur ya tsere sai a wajajen shekara 2013 aka kama shi a makabarta lokacinda yaje jana'izar mahaifiyarsa.
Kamfanin dillancin labarai NAN ya ruwaito Alkalin ya basu damar daukaka kara a cikin kwanaki 90.
HANAN BUHARI BA TA SOCIAL MEDIA
Ba ni da 'Account a shafin Social Media,' inji Hanan Muhammadu Buhari - Daga M INUWA MH ISMOG
Bayan auren Zahra Buhari jama'ar Nijeriya hankulansu ya karkata zuwa ga Hannatu Muhammad Buhari wadda ita ma 'ya ce ga shugaban kasa Buhari.
Saidai abin mamakin shine yadda yanzu 'yan social media suke ta kirkire-kirkiren account na Facebook da sunan Hanan Muhammad Buhari din saboda tsabar iya 419.
Kafin auren Zahra buhari ba kowa bane ya san Hanan. Haka ya sa ba za ka taba ganin wani shafi na account nata a social media ba.
Amma yanzu kuwa tunda aka nunata a jaridu nake ta ganin account mai suna Hannan Buhari yana yawo a yanar gizo wai Hannah Buhari.
To Allah ya kyauta. Ya kamata jama'a su daina neman suna da sunan wani. Yin hakan babban kuskure ne domin yana da kyau ka tsaya inda Allah ya ajiye ka.
To Wallahi Hannatu ta ce ba ta da wani account da sunan mahaifinta a shafin social media. Amma tace tana chat ba kuma lallai bane a san Username dinta.
Da fatan za a kiyaye a kuma kula da 'yan 419.
Thursday, 29 December 2016
SHEKARAU YA CACCAKI BUHARI
Tsohon Gwamnan Jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau ya soki gwamnatin jam’iyyar APC inda ya ce gwamnati mai ci ta gaza wurin cika alkawuran da Shugaba Buhari ya yi lokacin gangamin zaben shekarar 2015.
Shekarau ya kara da cewa, a cikin watanni 19 na mulkin jam’iyyar APC ba bu wani abu akasa da aka yi wa ‘yan Nijeriya, don haka gwamnati mai ci ta dai na sukar gwamnatin PDP saboda ta yi rawar gani.
Wednesday, 28 December 2016
ASALIN BATUREN DA AKA KAMA A SAMBISA
An Gano Asalin Baturen Da Aka Kama A Dajin
Sambisa Da Kuma Aikinsa
________¥__________ Rahotanni sun tabbatar da cewa Baturen da sojojin.
Nijeriya suka kama a Dajin Sambisa, dan asalin
kasar Faransa ne kuma ya kware ne wajen gyaran
manyan tankokin yaki da kuma yadda ake sarrafa
makamai. Wata majiyar tsaro ta nuna cewa an cafke Baturen
ne a yankin Bama inda ya nemi bayar da hadin kai
wajen bayar da Cikakkun bayanai game da
alakarsa da kungiyar. Gwamnatin Nijeriya ta ki
bayyana asalin Baturen ne saboda dalilan tsarin
diflomasiyya.
Tuesday, 27 December 2016
ZA A SAI DA MAI KAN N87 A JANUARY
Kara min ministan man fetur Emmanuel Ibe Kachukwu, ya ce za a saida man fetur akan kasa da naira 87 daga watan Janairu mai zuwa.
A lokacin da yake magana a matatan man futur na Port Harcourt.
Ya ce tuni ya sanya hannu a kudurin na rage kudin na man da zai fara aiki daga farkon shekara ta 2017.
Kachukwu, ya ce wannan na zuwa ne bayan cire duk karin wasu kudade da ake biya wajen sayen man.
Monday, 26 December 2016
HOTUNAN MUTANE DAKE KOMAWA GIDAJEN SU A BORNO
Sama da mutane 3,000 ne suka koma Damasak a jihar Borno
Sama da marasa galihu da yan gudun hijira 3,000 ne suka koma gidajensu tare da iyalansu bayan an fatattaki yan ta'addan Boko Haram daga dajin Sambisa.
Zasu kasance tare da dakarun sojojin Operation Lafiya Dole karkashin jagorancin Tukur Buratai.
ALLAH MAI RAHAMA: HOTUNAN KABARIN WANI MALAMI
Wani babban Malamin addinin Musulunci, ya rasu a Indonesia anje rufe shi kabarinshi ya cika da haske.
Allah kasa mu gama da Dunia lafia Allah ka haskaka mana kabarin mu.
BISA GA DUKKAN ALAMU KARSHEN ISRA'ILA YA ZO KARSHE
Tun bayan da Majalisar Dinkin Duniya ta jefa kuri'ar nuna rashin goyon bayan game da mamayar da Isra'ila ke wa yankunan Falasdinawa hankalin Yahudawa ya tashi inda firaminista Benjamin Netanyahu ya zargi Amurka da kulla musu sharri.
Netanyahu ya gaiyaci jakadan Amurka a Isra'ila don ta ba su bayanai kan dalilin da ya sa Amurka ta juya musu baya a wannan lokaci.
A ranar Juma'a ne Majalisar Dinkin Duniya ta jefa kuri'a don hana Isra'ila gine-gine a yankunan Falasdinmawa da ke Kudus da Yammacin Gabar Kogin Jordan.
A yayin jefa kuri'ar Amurka ta ba ta jefa kuri'a ba wanda hakan ya sanya Isra'ila ta ke zarginta da kulla mata sharri.
HOTUNA: HARIN KUDANCIN KADUNA
Kadan daga cikin hotunan harin da wasu 'yan ta'adda suka kai kudancin Kaduna, kenan.
Cikin su har da 'yar tsohon shugaban karamar hukumar Jema'a...
HOTUNAN 'YAR KUNAN BAKIN WAKE
Wata 'yar kunan bakin wake ta kashe kanta a harin wani Bam da ta kai da safiyar yau akasuwar shanu dake Maidugurin jihar Borno.
Rahotanni sun ce ba wanda ya rasa ransa ko ya jikkata, a harin...
Allah ya kyauta...
ALLAH YA YI WA RAHAMA RASUWA
Innalillahi Wa'inna Ilaihirrajiun...
Allah ya yiwa Rahama Haruna wacce ta dade tana rayuwa a cikin bahon roba, sakamakon nakasa da take da ita rasuwa.
Rahama ta rasu ne tana da shekaru 19 da haihuwa sakamakon gajeruwar rashin lafiya da tayi fama da ita.
Ta rasu ranar Lahadi 25 ga watan nan na December.
Allah yaji kanta da Rahama...
Amen....
KUDANCIN KADUNA: EL-RUFAI YA YI ALLAH WADAI DA HARIN 'YAN TA'ADDA
Gwamnan jihar jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya yi Allah wadai da sabon harin da 'yan ta'adda suka kai kauyakun Goska, da Kaninkon a karamar hukumar Jema'a.
Bayanin hakan ya fito ne ta bakin mai magana da yawun gwamnan Samuel Aruwan.
Gwamnan ya kuma nuna damuwa bisa rashin imanin mutanen dake aikata irin wadannan munanan ayyuka.
Ya ce gwamnatin jihar na yin dukkanin mai yiwuwa dan ganin an shawo kan wannan matsala.
An kai hare-haren ne ranakun Asabar da kuma Lahadin da suka gabata, inda suka kashe mutane da dama ciki har da mata da kuma yara.
Wannan na zuwa ne duk da dokar hana fita da aka sa a yankin, sakamakon tsoron barkewar rikici.
Saturday, 24 December 2016
RONALDO YA JINJINAWA YARAN SYRIA
Shahararren dan wasan nan da ya fi kowani dan wasa yin fice a bana Cristiano Ronaldo, ya ce yaran Syria da suka dade suna shan bakar wahala jaruman gaske ne.
Dan wasan na kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ya fadi hakan ne bayan da ya shiga kamfe din samar masu da abinci da magunguna da taimaka wa yaran Aleppo wadanda yaki ya shafa.
Ronaldo a wani faifan bidiyo da ya fitar a kafar sada zumunta ya ce, sun san da cewar mazauna yankin na shan bakar wahala.
Ronaldo ya kara da yin kira ga yaran da kada su yanke-kauna ko fidda rai, duniya tana tare da su, sannan shima yana tare da su.
A nashi jawabin wani babban jami’in kungiyar dake rajin kare hakkin yara save the Children, ya ce Ronaldo ba a bangaren taka leda kawai ya yi fice ba, ya shahara wajen taimakon mutane dake fama da wahalhalu.
Kungiyar ta ce ak alla yara dubu 15, aka kashe a cikin mutane sama da dubu dari 3 da suka rasa rayukan su a lokacin rikicin Syria da aka kwashe tsawon shekaru biyar ana yi a kasar.