SHINKAFAR ROBA: AKWAI BUKATAR MU MAIDA HANKALI
Ga bisa dukkan alamu, mun dade muna cin shinkafar roba, ba tare da mun sani ba, domin ko, Hukumar hana fasa kwauri ta Nigeria kwastam, ta ce ta kama buhuna 102 na wata shinkafar da aka yi da roba, wacce aka shigo da ita ta barauniyar hanya.
Wani babban jami'in hukumar ya ce wani dan kasuwa ne ya shigo da shinkafar domin sai da ita a cikin wannan lokaci na bukukuwan Kirsimati.
Jami'in mai kula da shiyya ta daya ta hukumar hana fasa kwauri da ke Ikeja Haruna Mamudu, ya ce binciken farko ya nuna cewa shinakafar ta roba tana cabewa idan an tafasa ta, sanan ya ce Allah ne kadai ya san irin illar da za ta yi wa duk wanda ya ci.
No comments:
Post a Comment