Shahararren dan wasan nan da ya fi kowani dan wasa yin fice a bana Cristiano Ronaldo, ya ce yaran Syria da suka dade suna shan bakar wahala jaruman gaske ne.
Dan wasan na kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ya fadi hakan ne bayan da ya shiga kamfe din samar masu da abinci da magunguna da taimaka wa yaran Aleppo wadanda yaki ya shafa.
Ronaldo a wani faifan bidiyo da ya fitar a kafar sada zumunta ya ce, sun san da cewar mazauna yankin na shan bakar wahala.
Ronaldo ya kara da yin kira ga yaran da kada su yanke-kauna ko fidda rai, duniya tana tare da su, sannan shima yana tare da su.
A nashi jawabin wani babban jami’in kungiyar dake rajin kare hakkin yara save the Children, ya ce Ronaldo ba a bangaren taka leda kawai ya yi fice ba, ya shahara wajen taimakon mutane dake fama da wahalhalu.
Kungiyar ta ce ak alla yara dubu 15, aka kashe a cikin mutane sama da dubu dari 3 da suka rasa rayukan su a lokacin rikicin Syria da aka kwashe tsawon shekaru biyar ana yi a kasar.
No comments:
Post a Comment