Rahotanin sun tabbatar da cewa wani dan sandan kwantar da tarzoma, ya kashe wasu mutane biyu a kusa da Bankin Zenith dake Zaria, dake Kaduna Najeriya.
Lamarin ya auku ne da misalin karfe 10 zuwa 11 na ranar Juma'ar nan.
Shaidun gani da ido, sun ce dan sandan ya samu rashin jituwa ne da wasu daban, inda daga bisani ya fito daga cikin mota da bindiga tare da yin harbin kan mai uwa da wabi, inda a nan take ya kashe wani mai Keke Napep, da kuma wani mutum guda.
Har ila yau, mutane da dama sun jikkata, inda wasu suka ji rauni a lokacin da suke gudu domin tsira da rayukan su.
Allah ya kyauta....
No comments:
Post a Comment