Saturday, 24 December 2016

KWALLON KAFA: NAJERIYA ZA TA ZABO WANDA ZAI WAKILCE TA A CAF


Gwamnatin tarayya ta kafa wani kwamiti dai zai tantance tare da zabo wanda ya kamata ya wakilci Najeriya, a zaben wakilan kwamitin gudanarwa na hukumar kwallon kafa ta Afrika, wanda zai a yi shekara mai zuwa.
Daya daga cikin mutanen da suka gabatar da aniyar su ga gwamnatin tarayya shine Amaju Pinnick, duk da cewa gwamnatin ba ta bashi tabbas, ga bukatar ta sa ba.
Ministan kula da harkokin matasa da wasanni Solomon Dalung, ya ce har yanzu Najeriya ba ta tantance wanda ya kamata ta tura da sunan sa ba, adon haka ne ta kafa kwamiti na musamman, domin gudun kar ta yi zaben tumin dare.
Mutane da dama ne dai a bangaren wasanni, suka nuna sha’awar su na, shiga cikin wadanda za su wakilci Najeriya a zaben da za a gudanar a watan Maris din shekara ta 2017.

No comments:

Post a Comment