Gwamnan jihar jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya yi Allah wadai da sabon harin da 'yan ta'adda suka kai kauyakun Goska, da Kaninkon a karamar hukumar Jema'a.
Bayanin hakan ya fito ne ta bakin mai magana da yawun gwamnan Samuel Aruwan.
Gwamnan ya kuma nuna damuwa bisa rashin imanin mutanen dake aikata irin wadannan munanan ayyuka.
Ya ce gwamnatin jihar na yin dukkanin mai yiwuwa dan ganin an shawo kan wannan matsala.
An kai hare-haren ne ranakun Asabar da kuma Lahadin da suka gabata, inda suka kashe mutane da dama ciki har da mata da kuma yara.
Wannan na zuwa ne duk da dokar hana fita da aka sa a yankin, sakamakon tsoron barkewar rikici.
This blog is a blog that keeps you informed of local and international news, Events, and Issues, happenings around the world, including entertainments, it breaks the news while its hot.
Monday, 26 December 2016
KUDANCIN KADUNA: EL-RUFAI YA YI ALLAH WADAI DA HARIN 'YAN TA'ADDA
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment