Rundunar Sojin Najeriya ta kubutar da karin mutane 1,880, da Boko Haram, ta yi garkuwa da su a dajin Sambisa.
Kwamandan runduna ta musamman Operation Lafiya Dole, dake yaki da ayyukan ta'addanci a Arewa maso gabas mai Maj.-Gen. Lucky Irabor, ya tabbatar da haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a barikin soji na Maimalari, dake Maiduguri babban birnin jihar Borno.
Ya kara da cewa rundunar ta kuma kama wasu 'yan Boko Haram 504, yayin da wasu 19 suka mika wuta.
Ya ce rundunar ta kuma kama wasu 'yan kasashen ketare 37, da take kyautata zaton 'yan ta'adda ne.
Har ila yau ta kuma kama masu garkuwa da mutane 7, wanda yanzu haka take gudanar da bincike akan su.
No comments:
Post a Comment