Friday, 23 December 2016

NAJERIYA ZA TA SAMU SABON DAN WASAN GABA

Wannan matashin dan wasan kwallon kafar na kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, dake kwallon taka leda na wucin gadi yanzu haka a kungiyar kwallon kafa ta Bristol City, Tammy Abraham, ya jinkirta zaben kasar da zai rika wakilta wajen taka leda.

A halin yanzu dai Najeriya da kasar Burtaniya ne ke zawarcin dan wasan, inda dukkanin su ke burin ganin dan wasan ya amince da ita.


Chelsea loanee Tammy Abraham has delayed a decision regarding his international future with the Nigeria Football Federation and English FA interested in his services.

Sai dai wani daya daga cikin masu ruwa da tsaki na hukumar kwallon kafa ta Najeriya Amaju Pinnick, wanda yake da kusanci matuka da mahaifin dan wasan, ya ce yana da tabbacin dan wasan zai zabi Najeriya akan kasar Burtaniya. 

A nashi jawabin, dan wasan gaban ya ce, duk da yake ba yanzu ne dai-dai lokacin da ya kamata ya yi magana akan wannan batu ba, burinsa shine ya kasance daga cikin 'yan wasa da ake yi dasu koda yaushe a duk kasar da ya zaba.

A bangare guda kuma mataimakin shugaban hukumar kwallon kafa ta Najeriya, ya ce ana sa ran dan wasan zai fara bugawa Najeriya kwallo, a wasan da za ta yi da kasar Kamaru, na cancantar shiga gasar cin kofin duniya. 

No comments:

Post a Comment