Kungiyar kwallon kafa ta Najeria ta samu koma baya a jerin kasashen da suka fi iya kwallo.
A jerin kasashen da hukumar kwallon kafa ta duniya ta fitar dai Najeriya ce ta 51, wajen iya kwallo a duniya, yayin da take na 8 a Afrika.
Wannan ke nuna cewa Najeriya zata kammala shekara ta 2016, cikin kasashen 10, da suka fi kowa iya taka Leda a Afrika, duk da gazawa da ta yi wajen samun tikitin shiga cikin jerin kasashen da za su fafata a gasar cin kofin zakarun Afrika na 2017, wanda zai gudana a Gabon.
So guda Najeriya dai ta taba zama ta biyar a Afrika, sakamakon irin rawar da ta taka a gasar cin kofin duniya na shekara ta 1994.
A halin yanzu kasashen Senegal, Ivory Coast, Tunisia, Egypt da Algeria, dai su ke matsayi na daya zuwa biyar, yayin da kasar Argentina ke matsayi na 1 a duniya.
No comments:
Post a Comment