Thursday, 22 December 2016

GABON BA ZA TA SHIGA FINAFINAN AMURKA BA - GORA II

GABON BA ZA TA SHIGA FINAFINAN AMURKA BA - GORA II

Shahararren Editan nan na Mujallun fina-finai da ya yi aiki, da 'yan wasan Hausa da dama, Aliyu Abdullahi Gora II, ya ce Hadiza Gabon bata da ninyan shiga harkar fina-finai, shi yasa ta yi furucin barinta ta sanya Hijabi a masana'antar shirya Fim na kasar Amurka (Hollywood).

Sir Gorah, ya ce babban makasudin furucin na Hadiza Gabon shine ta sanar da masoyan harkar fina-finai cewa ba za ta taba, amsa gayyatar Hollywood ba, koda sun gayyace ta a nan gaba.

Ya ce shahararriyar 'yar wasan, ta san cewa addini da al'adar ta basu bata daman yin wasu abubuwa da ake yi a masana'antar ta Hollywood ba.

Wannan na zuwa ne biyo bayan furucin da Hadiza Gabon ta yi na cewa za ta amince da shiga harkar shirya fina-finai na kasar Amurka matukar za a bar ta ta sanya Hijabi.




1 comment:

  1. Gaskiyya da za a samu irin wadannan a kannywood da an samu cigaba a harkan fina-finai na kannywood.

    ReplyDelete