GABON BA ZA TA SHIGA FINAFINAN AMURKA BA - GORA II
Shahararren Editan nan na Mujallun fina-finai da ya yi aiki, da 'yan wasan Hausa da dama, Aliyu Abdullahi Gora II, ya ce Hadiza Gabon bata da ninyan shiga harkar fina-finai, shi yasa ta yi furucin barinta ta sanya Hijabi a masana'antar shirya Fim na kasar Amurka (Hollywood).
Sir Gorah, ya ce babban makasudin furucin na Hadiza Gabon shine ta sanar da masoyan harkar fina-finai cewa ba za ta taba, amsa gayyatar Hollywood ba, koda sun gayyace ta a nan gaba.
Ya ce shahararriyar 'yar wasan, ta san cewa addini da al'adar ta basu bata daman yin wasu abubuwa da ake yi a masana'antar ta Hollywood ba.
Wannan na zuwa ne biyo bayan furucin da Hadiza Gabon ta yi na cewa za ta amince da shiga harkar shirya fina-finai na kasar Amurka matukar za a bar ta ta sanya Hijabi.
Gaskiyya da za a samu irin wadannan a kannywood da an samu cigaba a harkan fina-finai na kannywood.
ReplyDelete