Tsohon Captain na kungiyar kwallon kafa ta Najeriya, Daniel Omokachi, ya zargi wasu wakilan 'yan wasa da ba Koca-Kocan Najeriya kudi domin gayyatar 'yan wasan su, a duk lokacin da Super Eagles ta ke da wasa.
Duk da cewa ba wani da aka taba kamawa da hannu a irin wannan aika-aika, an dade ana zargin irin wannan badakala a kungiyar Kwallon kafar.
Omokachi dai ya yi aiki a matsayin mataimakin mai horas da kungiyar a lokacin da Stephen Keshi, ke jagoranta a shekara ta 2011 zuwa 2015, sannan ya yi aiki da Austin Eguavoen, da kuma Shuaibu Amadu.
Ya ce dukkanin masu horas da kungiyar da ya yi aiki dasu, sun dade suna kokawa kan batun.
A karshe ya bukaci hukumomin da abin ya shafa, da su dau matakan da suka kamata, don gudanar da bincike akan wannan badakala.

No comments:
Post a Comment