Jaruma Finafinan Hausa sun soma rige-rigen kafa gidauniyoyi da zummar tallafa wa jama'ar dake bukatar taimako.
Daya daga cikin su, Hadiza Gabon, ta shaida wa manema labarai cewa suna yin hakan ne "domin nuna godiya ga Allah bisa baiwar da ya yi mana, sannan mu nunawa marasa karfi cewa Allah yana tare da su."
Ita dai wannan jaruma ta bayar da tallafi sau da dama ga 'yan gudun hijirar da suka bar gidajensu sakamakon hare-haren kungiyar Boko Haram, wadanda yanzu haka suke sansanonin 'yan gudun hijira.
Baya ga haka, tana taimaka wa daliban kananan makarantu da litattafai da sauran kayan koyon karatu.
A cewar jarumin, gidauniyar za ta rika bayar da taimako ga marasa galihu da marasa lafiya da 'yan gudun hijira da marayu da zawarawa.
Zango ya ce zai samu kudin gudanar da gidauniyar ne ta hanyar shirya bikin rawa a dukkan jihohin Najeriya wanda zai soma a watan Janairu mai zuwa.
'Samarwa matasa mafita'
Shi kuwa Ali Nuhu, ya shaida wa BBC cewa kodayake bai kafa gidauniya a zahiri ba, amma babban abin da ya sanya a gaba shi ne taimakawa matasa domin su rika tsayawa da kafafunsu.
A cewar jarumin, hakan zai rage matsalar rashin aikin yin da ake fama da ita a Najeriya.
"Ni dai ba ni da gidauniya, amma ina sanya matasa a fina-finan da nake yi domin su samu abin da za su rika kula da kansu", in ji jarumin.
'Nuna ƙauna'
Gidauniyar, mai suna The Love Laugh Foundation, za ta mayar da hankali ne kan nuna kauna da tallafi ga marasa galihu da mata da marayu da 'yan gudun hijira.
A kwanakin baya jarumar ta shirya wani biki a birnin Kaduna inda aka tara miliyoyin kudaden da ta ce za ta yi amfani da su wajen tallafawa 'yan gudun hijira da sauran mutanen da ke cikin mawuyacin hali.
Masana abubuwan da ke faruwa a Kannywood sun yi san-barka ga wannan kokari da jaruman ke yi na taimaka wa al'uma.
Malam Ibrahim Sheme, wanda ya dade yana tsokaci kan Kanyywood, ya ce matakin zai inganta dangantakar da ke tsakanin jaruman da al'umar da ke yi musu kallo a matsayin masu wargaza tarbiyya.
Ya kara da cewa, "Wannan mataki yana da kyau amma ina ganin ba shi da tsari. Ya kamata jarumai kamar goma wadanda ke da irin wannan aniya su hada kungiya da za ta rika aiwatar da irin wannan shiri, ba kowa ya yi gaban kansa ba."
"Za su iya yin amfani da kungiyar wajen neman taimako a wurin manyan attajirai irin su Aliko Dangote da kuma kasashen duniya.
Irin hakan ne ke faruwa a Hollywood, inda za ka ga jarumai sun zama jakadun wasu kamfanoni ta yadda za su rika yin amfani da matsayinsu suna nema wa al'uma, musamman mutanen da ba su da galihu taimako, in ji Malam Sheme.
Sai dai ya ce duk da haka abin da suke yi yana da matukar muhimmanci wajen sauya akalar tunanin mutanen da ke yi musu kallo irin na masu son tozartar al'adu da dabi'un al'uma.
Wani batu kuma da masu sharhi suke zuba ido su gani shi ne tasirin wannan yunkuri na jaruman kan irin kallon da jama'a suke yi fagen fim din.
'Yan Kannywood dai suna fuskantar suka daga wasu bangarorin al'umma kan cewa suna bata tarbiyyar jama'a, abin da suka sha musantawa a lokuta daban-daban.
No comments:
Post a Comment