Thursday, 22 December 2016

ANICHEBE BAI SHIRYA BUGAWA NAJERIYA BA



ANICHEBE ZAI BUGAWA NAJERIYA, AMMA BA YANZU BA –
MOYES

Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Sunderland dake kasar Burtaniya David Moyes, ya ce shahararren dan wasan kungiyar Victor Anichebe, zai shirya komowa kungiyar kwallon kafa ta Najeriya Super Eagles ba.
Wannan na zuwa ne, sakamakon irin rawar da Anichebe, ya taka tun bayan lokacin da ya koma kungiyar.
Moyes, ya ce dan wasan zai so ya ba kungiyar ta Super Eagles gudunmawa, amma ba yanzu ba, sai nan gaba.
Anichebe wanda ya bugawa kungiyar Everton a baya, ya zurawa kungiyar kwallaye 3 a raga cikin wasanni 17, da ya buga a kakar gasa Premier na kasar Burtaniya.
Sannan ya taba bugawa Najeriya a gasar cin kofin zakarun Afrika a shekara ta 2012, inda ya buga wasan sa na karshe a karawar da Najeriya ta yi da Madagascar. 



No comments:

Post a Comment