Dakarun kungiyar rainon kasashen yammacin Afirka, na cikin shirin ko-ta-kwana domin kawar da Yahaya Jammeh na Gambia daga mulki muddin yaki sauka daga kan karagar mulki a ranar 19 ga watan Janairun shekara ta 2017.
Shugaban kungiyar ta ECOWAS, Marcel de Souza, ya ce sun jibge jami’an tsaron ne da Senegal ke jagoranci, domin ba za su zura ido a danne hakkin mutanen a kasar Gambian ba.
Jammeh da bai tanka wannan batu ba, a baya ya ce Ecowas bata da ikon tsoma baki kan harkokin siyasa na cikin gidan Gambia.
Sai dai suma gamayar ‘yan adawar kasar sun lashi takobin gani lallai an rantsar da zabebben shugaba Adama Barrow a watan gobe.
A cewar ‘yan adawa ba zasu saurare hukunci kotu ba, kuma tabbas Barrow na da kwarin-gwiwar shi ya lashe zabe, don haka babu wata kotu a duniya da za ta yanke hukunci sabanni haka.
No comments:
Post a Comment