DOMINKI NE DA MIJINKI
ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮﺣﻴﻢ
ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﺁﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﻭﺳﻠﻢ
ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﺁﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﻭﺳﻠﻢ
Daga cikin sifofin miji na qwarai ya zama mai matuqar sha'awar ganin abokiyar rayuwarsa kowani lokaci, ya yi fatan magana da ita koda yaushe, ya riqa debe mata haso shi ma yadebe na sa, ba wai ya ajiye ta kamar gadonsa da in ya debo gajiyarsa sai ya hau don ya kawar ba, wanda in ya gama ya sauka domin shiga wata sabgar ta daban ba tare da ya yi tunanin gadon ba.
Kai madalla da miji na qwarai wanda ya yi aure mai albarka, ya sami kyakkyawar zamantakewa da iyalinsa, har ya kasance matarsa tana alfahari da shi, a maimakon jin tsoronsa, ya zama duk wani shirgi na ta za ta iya gaya masa cikin kwanciyar hankali tare da zaton zai saurare ta.
Maigida na qwarai yakan so su riqa ambaton Allah shi da iyalinsa, ya koya mata yi masa addu'a, ya riqa zama da ita suna tattauna matsalolinsu, wannan zaman zama ne na masoya, masu qaunar junansu, masu manufa iri guda wato ci-gaban iyalin da kare shi.
A nan za ka ga murmushi koda yaushe a gaban iyalinsa, wanda shi ne yake dauwama har kullum a zuciyarta ta yi ta fatar dawowarsa don ta sake ganin wannan murmushin, wallahi kyawun murmushinsa ya fiye ma ta tufafin da yake sakawa, in ka yi wa wani qato murmushi sadaqa ne, to ya kake ganin cewa in ka yi wa iyalinka da kullum take begenka har sai ka dawo gare ta?
Miji na qwarai yakan yi qoqarin yi wa iyalinsa adalci, yakan ji cewa tana da haqqoqi a kansa kamar yadda yake da su a kanta, don haka ne ma yake fatar farin cikinta kamar yadda shi ma take masa.
Wani dadi za ka ji in kaga iyalinka tana binka a baya lokacin da za ka fita tana yi maka addu'a cikin fara'a da qaunar saduwa, kana dawowa ta tarbo ka cikin murna da jin dadi?
Shin ka sakar ma ta fuska da za ta sami wannan a wurinka?
Ko kana jira a yi mata wahayi ne daga sama cewa ga abin da za ki yi wa mijinki?
Yalla6ai kai ne mai gyara gidanka da kanka fara tun daga yau.
Haquri da yi wa mace rangwame dabi'a ce ta maigida na qwarai, yakan yi haquri ya yafe mata duk lokacin da ta yi masa wauta, tare da sanin cewa za fa ta qara wani kuma dole dai ya kuma jurewa, da za ka kai qarar mace wurin mahaifinta za ka taras shi ma haquri yake yi da mahaifiyarta, in ka sake ta ka auro wata, to akwai buqatar ka fara tara kudin auro wata kuma, gama dai duk sunayensu mata.
Tabbas mace ba ta ji, to kai ina na ka hankalin?
Idan ita ta yi shirme kai kuma me ka yi?
Shi ya sa sakin fuska da murmushi da tarairaya da kulawa yakan yi mu'ujizar da daurewa da 6ata rai ba sa yi, ka yi qoqarin samun hanyoyin da za ka kusanto da iyalinka jikinka, ka ba ta damar da za ta riqa tuntu6arka a duk abin da ta yi niyyar aikatawa.
Kar ka sake ka riqa gwasale ta sai ta nisance ka, duk abin da ta yi niyya za ta aikata ne ba sai ta tuntu6e ka ba, don ta san abin da za ka yi mata, wannan sakewa da mu'amalla da iyali zai sa har 'ya'yanka su riqa kusantarka, ko da yake zaki ba ya zama tare da yaransa ko matansa sai dai uwaye mata, to ai shi dabba ne, kai kuwa mutun ne da Allah ya hada maka komai da dan adam yake buqata.
Ashe ba muga hadisin da Annabi ya kwanta a cinyar iyalinsa yana barci ba yayin 6acewar tsakiyarta?
Yaushe kai za ka kwanta a cinyar ta ka iyalin?
Mata suna da tarin jahilci na rashin iya zama da mazajensu, haka maza suke da tarin gidadanci wajen tafiyar da matayensu don me kuwa saki ba zai yawaita a matattararmu ba?
YANZU DAI MU FARA NEMO HANYOYIN GYARA.
YANZU DAI MU FARA NEMO HANYOYIN GYARA.
Zamu ci gaba insha Allah
...
...
No comments:
Post a Comment