Wani mutum dan shekaru 56, da haihuwa, wanda ke wa'azi a wani Coci, dake yankin Obodo, a jihar Ondo ya yi wa 'yar sa, yar shekara 16, ciki.
Mutumin wanda yanzu haka ke fuskantar bincike a wajen 'yan sanda, ya ce shedan ne ya ingiza shi har ya aikata wannan aikata-aika.
Wasu mazauna Unguwar, sun shaida cewa, mutumin ya yi hakan ne, domin kara karfin ayyukan siddabaru da yake yi.
Malamin addinin Kiristan dai ya shahara, wajen yiwa mata a kududdufi, wanka domin korar shaidanun da suka hana su aure.
Rahotanni sun ce a kwanakin baya ne, Faston ya rabu da matarsa, inda ta yi kokarin daukan yarinyar ta tafi da ita, amma mutumin ya hana.
No comments:
Post a Comment