Wednesday, 21 December 2016

MA'AIKATA ZA SU SAMU ALBASHIN SU - MINISTAR KUDI

ALBASHIN MA'AIKATA NA WANNAN WATAN

Gwamnatin tarayya ta daura alhakin jinkiri da aka samu wajen biyan Ma'aikata kan wasu shugabannin hukumomin.

Ministar kudi Kemi Adeosun ta tabbatar da haka a lokacin da take zantawa da manema labarai na fadar shugaban kasa dake Abuja.

Ta ce shugabannin hukumomin ba suyi amfani da ku daden yanda ya kamata ba, shi yasa kudaden Albashin suka kare kafin wannan Watan.

Adeosun, ta ce da yawan hukumomin, suna amfani da kudaden ne da aka ware domin biyan albashi, kan wasu abubuwa na daban.

A karshe ta ce nan bada jimawa ba za a biya ma'aikatan da ba a biya su albashin su na wannan watan ba.

No comments:

Post a Comment