Friday, 30 December 2016

ZA A RATAYE DAN HAKIMI A KATSINA


An yankewa wani dan Hakimin Katsina hukuncin kisa ta hanyar rataya

Wata babbar Kotu dake Funtua a jihar Katsina ta yankewa, Mu’ammar Tukur dan mai martaba tsohon hakimin Bakori hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa samun shi da laifin kisa.

Kotun ta kuma ce bata da hurumin yin sassauci akan hukuncin.

Tukur mai shekara 32, wanda kuma margayi mahaifin nasa ya wakilci Bakori da Danja a majalisar wakilai ta tarayya, kotu ta same shi da laifin dabawa Shafir Muktar wuka a ranar 21 ga watan Afrelun 2008 a gidan kallo.

Da yake yanke hukunci a ranar Alhamis Alkalin kotun mai Shara'a, Abbas Bawale ya ce kotu ta samu gamsassun shaidu da hujjoji da suka tabbatar da shine yayi kisan.

Hausa Times ta samu bayanin tun bayan faruwar kisan a shekara 2008 Tukur ya tsere sai a wajajen shekara 2013 aka kama shi a makabarta lokacinda yaje jana'izar mahaifiyarsa.

Kamfanin dillancin labarai NAN ya ruwaito Alkalin ya basu damar daukaka kara a cikin kwanaki 90.

No comments:

Post a Comment