Monday, 26 December 2016

BISA GA DUKKAN ALAMU KARSHEN ISRA'ILA YA ZO KARSHE


Tun bayan da Majalisar Dinkin Duniya ta jefa kuri'ar nuna rashin goyon bayan game da mamayar da Isra'ila ke wa yankunan Falasdinawa hankalin Yahudawa ya tashi inda firaminista Benjamin Netanyahu ya zargi Amurka da kulla musu sharri.

Netanyahu ya gaiyaci jakadan Amurka a Isra'ila don ta ba su bayanai kan dalilin da ya sa Amurka ta juya musu baya a wannan lokaci.

A ranar Juma'a ne Majalisar Dinkin Duniya ta jefa kuri'a don hana Isra'ila gine-gine a yankunan Falasdinmawa da ke Kudus da Yammacin Gabar Kogin Jordan.

A yayin jefa kuri'ar Amurka ta ba ta jefa kuri'a ba wanda hakan ya sanya Isra'ila ta ke zarginta da kulla mata sharri.

No comments:

Post a Comment