Friday, 30 December 2016

ASALIN BATUN ADDININ RAHAMA SADAU


Rahma Sadau, ta ce tana nan daram a cikin addinin Musulunci.

Jarumar ta bayyana hakan ne sakamakon jita-jitar da ake ta yadawa na cewa ta bar Musulunci bayan an yaudare ta da dalolin miliyoyin kudi na Amurka.


Idan ba a mance ba dai, Rahma Sadau ta koma kasar Amurka ne sakamakon gayyatar da shahararren mawakin kasar Amurka Akon da wasu suka yi mata, sakamakon korar ta da aka yi daga masana'antar fim bayan an zarge ta rungumar wani mawaki mai suna Klassiq a wata kasarsa ta bidiyo.

No comments:

Post a Comment